Sakataren harkokin wajen Amirka ya fara ziyarar kwanaki biyu a Alkahira
September 13, 2014Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry wanda ya isa birnin Alkahira a wannan Asabar don fara ziyarar kwanaki biyu, zai tattauna batutuwan da suka shafi kasashen Amirka da Masar da kuma yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da barazanar da kungiyar IS ke wa kasashen Iraki da Siriya. Kerry ya ce Masar da ake wa kallon cibiyar kasashen Larabawa, tana da muhimmiyar rawa da za ta taka wajen yaki da akidar kungiyar IS mai da'awar kafa daular Islama.
"A matsayin babbar cibiyar masu ilimi da al'adu na duniyar Musulmi, Masar na da muhimmiyar rawa da za ta taka wajen magance akidojin tsattsauran ra'ayi irin wanda ISIL ke yadawa. Wannan na daga cikin batutuwan da muka tattauna a birnin Jeddah, wanda kuma za mu tattauna a nan birnin Alkahira.
Kerry na rangadin kasashen yankin ne don samun goyon baya ga shirin Amirka na kulla wani kawancen yaki da kungiyar IS.