SiyasaAsiya
Bude iyaka tsakanin Katar da Saudiyya
January 9, 2021Talla
Rahotanni daga birnin Riyadh fadar gwamnatin Saudiyya na nuni da cewa motocin Katar sun fara shiga Saudiyyan ta kan iyakar kasar biyu, kwanaki kalilan bayan Saudiyya ta kawo karshen rufe kan iyakokinta ga Katar, a wani mataki na mayar da Doha saniyar ware a yankin Gabas ta Tsakiya.
Jagororin wasu kasashen Larabawa wato Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Bahrain har da Masar, sun sanya hannu kan yarjejeniya da Qatar din yayin taron kungiyar kasashen yankin Gulf, a wani mataki na kawo karshen zaman doya da manjar da kasashen ke yi da Qatar har tsawon sama da shekaru uku. Ita ma dai Hadaddiyar Daular Larabawa, za ta bi sahun Saudiyya wajen bude kan iyakokinta na kasa da na sama da ma na ruwa ga Qatar.