Yamutsi a Isra'ila saboda canza doka
March 12, 2023Talla
Kafofin yada labarai na Isra'ila sun rawaito cewar sama da mutane dubu dari sun halarci gangamin a tsakiyyar birnn Tel Aviv saboda gwamnatin Benjamin Netanyahu na shirin gaggauta aiwatar da ayyukan majalisar dokoki a yau Lahadi, ranar farko ta mako a Isra'ila, don ingiza wannan shiri na sauye-sauye tsarin sharia a kasar. Wannan garambawul na alamuran sharia a israila zai baiwa gwamnatin ikon nada alkalai a maimakon kotun kolli, da kuma wasu sauye-sauyen abin da jamaa ke cewa taka tsarin dimukaradiyya ne