1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain: Sakonnin abubuwa masu fashewa

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 1, 2022

Wasu alamomi sun nunar da cewa ofishin jakadancin Ukraine a Spain da ke birnin Madrid, ya karbi wasu sakonni cikin ambulan dauke da abubuwa masu fashewa.

https://p.dw.com/p/4KLXt
Spain  Madrid | Ukaraine | Ofishin Jakadanci | Sakonni | Abubuwa Masu Fashewa
Ofishin jakadancin Ukraine a Spain, ya karbi sakonnin abubuwa masu fashewaHoto: Europa Press/ABACA/picture alliance

Haka kuma rahotannin sun nunar da cewa, sakonnin da yawanassu ya kai biyar an tura su ga kamfanin kera makamai na Spain din da kuma wasu ofisoshi da hukumomin gwamnati. Tuni dai mataimakin ministan cikin gida na Spain din, Rafael Perez ya tabbatar da afkuwar lamaarin a wata hira da ya yi da manema labarai.