Salva Kiir na fiskantan matsi daga duniya
August 26, 2015Talla
Sa-hannun fatan da ake yi shi ne ya kawo karshen tashin hankali da aka fara kusan shekaru biyu, inda dubban mutane suka mutu, wasu sama da miliyan biyu suka rasa gidajensu. Tun kusan kwanaki 20 da suka gabata madugun 'yan tawayen Riek Macher ya sanya hanu kan yarjejeniyar, yayinda shi kuwa Salva kiir ya ce akai masa takardun ya yi nazari kafin sa hannu. Amirka dai a yanzu ta sa kahon zuka kan Juba, inda Amirkan ta gabatar da wani kuduri mai tsanani kan Sudan ta Kudu, wanda zai hada da hana sayar mata da makamai, muddin shugaba Salva kiir ya ki sa hannu.