1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samar da makamashi da ake sabuntawa a Afirka

Ahmed Salisu/GATDecember 2, 2015

Wasu kasashe da suka hada da Faransa da jamus na shirin bada kudade don samar da makamashi da ake sabuntawa a kasashen nahiyar Afirka a wani mataki na yaki da gurbatar muhalli.

https://p.dw.com/p/1HFqt
Indien deutsche Solarfirma Enerparc
Hoto: DW/K. Keppner

Wakilan kasashen Afirka da kungiyoyin da ke fafutukar kare muhalli wanda yanzu haka suke halartar taron sauyin yanayi a birnin Paris na kasar Faransa sun ce yunkurin da wasu kasashe ciki kuwa har da Faransa da Jamus suka yi na bada tallafin makudan kudade don samar da makamashi da ake sabuntawa kyakkyawar hanya ce ta magance abubuwan da ke haifar da sauyin yanayi a nahiyar.

Ga alama dai wannan yunkuri na Faransa da Jamus na bai wa Afirka kudaden masu yawan gaske domin bunkasa samar da makamashi a nahiyar musamman ma dai daga hasken rana da kuma iska na daya daga cikin labaran da suka faranta wa wakilan kasashen a wajen taron sauyin yanayi da a yanzu haka ake cigaba da gudanarwa a Faransa.

Kungiyoyin fafutkar kare muhalli a Afirka sun yaba da shirin:

Mohammed Adow guda daga cikin fitattun 'yan rajin kare muhalli a kasar Kenya ya ce wannan yunkuri wata hanya ce ta dakile irin abubuwan da ke taimakawa wajen yin illa ga muhalli wanda ke jawo sauyin yanayi a nahiyar Afirka.

Indien erneuerbare Energie Solarenergie in Punjab
Hoto: Getty Images/N. Nanu

"Wannan yunkuri bai tsaya ga samar da yawan makashin da nahiyar Afirka ke bukata ba, hakan na nufin dakile gurbata muhalli. Wannan na da matukar muhimmanci musamman ma a wannan lokacin da ke fama da illolin da sauyin yanayi ke haifarwa".

Wani lamari da har wa yau zai taimaki Afirka idan wannan tsari na bukasa makashi ya tabbata shi ne samar da aiki ga dumbin al'ummar Afirka wanda da dama suke zaman kashe wando, kana hakan zai taimaka wajen rage kwarara 'yan cirani daga nahiyar zuwa wasu nahiyoyin don neman aikin yi. Ingrid-Gabriela Hoven ta ma'aikatar raya kasa ta nan Tarayyar Jamus na daga cikin masu wannan hange.

"Afirka na da matasa da ke tsakanin shekaru 15 zuwa 25 da ke bukatar aikin yi to sai dai hakan bai samu. Matasan za su iya yin aiyyukan da za su yi dogaro da kansu a wurare da dama amma kafin a kai ga haka din suna bukatar makamashi".

A daura da wannan kalamai da Ms Hoven ta yi, muhawara ta kacame game da tafiyar da dorewar shirin samar da makamashin da ake sabuntawa a nahiyar ta Afirka don rage gurbata muhalli, inda bakin da dama daga cikin masu ruwa da tsaki ya zo daya kan cewar ya kyautu a shata hanyoyin da za a bi wajen tafiyar da wannan tsari don gudun kada ya durkushe har a kai ga komawa gidan jiya.

China Windenergie
Hoto: Getty Images/AFP/L. Jin

Ra'ayin ministar muhalli ta Najeriya kan wannan shiri:

A hannu guda kuma wasu wakilan Afirka din wajen taron sauyin yanayi na da ra'ayin cewar ita ma Afirka ya kamata ta bijiro da hanyoyi na killace muhallinta daga gurbacewa musamman ma dai magance kwararowar hamada a wasu sassan nahiyar wadda tuni ta yi ta'adin gaske ga gonaki da ruwa da ake amfani da su. Amina Mohammed ita ce minista muhalli a Najeriya.

 "Hamada ta yi ta'din gaske ga rayuwar mutane wadda hakan ya jawo talauci sosai. Yadda take karuwa da kusan kilomita biyu duk shekara a kasashenmu na nuna irin muhimmnacin da ke akwai na daukar matakai cikin gaggawa. Akwai bukatar gina shinge da kange hamada daga afka mana. Abu ne da ke bukatar hadin kai kana dole a dau lokaci ana yi. Ba abu ne da za a yi na shekaru uku a ce an bari ba".

Abin jira a gani dai yanzu haka shi ne irin yadda lamura za su kasance a cikin shekarun da ke tafe dangane da wannan batu da ma dai sauran matakai da za a gani nan gaba kan batun killace muhalli a duniya da nufin kawar da matsalar sauyin yanayi.