Samun ciki garari ga 'yan mata a Tanzaniya
February 27, 2018Tun a tsakiyar bara gwamnatin Shugaba John Magufuli, ta yi dokar haramta wa 'yan mata da ke dauke da ciki ci gaba da karatu, don haka a ke korarsu daga makaranta muddin suna da ciki.
Mahaifiyar Maidas Hassan Ilonga, wata jaririya ta bayyana yadda ita kanta 'yar shekaru 19 da haihuwa ke cikin taikaici tamkar ta barke da kuka:
"Har yanzu ina cike da takaici, duk da cewa yanzu na yi watanni da haifar diyata, amma har yanzu ina matukar son komawa makamaranta. Da ina da tsarin rayuwa da na yi."
Sai dai tsarin da tayi na rayuwar bai nasara ba, domin tana 'yar shekaru 18 ta samu ciki, tana dab da kammala karatunta. Ta ce wani saurayinta ne da yaudara, ya rufe ta a daki bata da karfin halin guduwa inda ya yi ta lalata da ita. Wannan matsalar dai ba mahaifiyar Maidas kawai ta shafa ba, a kasar Tanzaniya makarantu da yawa na yi wa 'yan makaranta mata gwajin ciki a duk wata guda, jim kadan bayan da uwar Maidas a ka yi mata gwaji ya nuna tana da ciki, sai kawai ga 'yan sanda sun so cikin ajinta:
"An tsareni inda a ka kaini ofishin 'yan sanda da ke wani gari kusa da mu. Sun bayyana min cewa sun kama ni domin ina da juna biyu, duk da cewa ban kammala karatu ba, sai suka rufeni a kurkuku."
Haramta ci gaba da karatu ga mata da ke dauke da ciki, a bara ne Shugaba John Magufuli wanda rikakken mai bin darikar Katolika ne ya sanya dokar, inda yace duk mahaifin da 'yarsa ta samu ciki bata kammala karatu ba, to a daure mahaifin tsawon shekaru 30 a gidan yari kamar yadda Sebastian Waryuba, daya daga cikin gwamnonin jihohion kasar ya tabbatar:
"Muna matukar son 'ya'yanmu su je makarantu, ta yadda za su kyautata makomar rayuwarsu. To amma idan 'yan mata na daukar ciki ya kamata dokoki su yi aiki a kansu."
A karshen watannin bara kawai bayan sa dokar, 'yan mata kimanin 55 suka bar makaranta sakamakon dokar da gwamnatin Tanzaniya ta sanya. Ga wasu mazajen da a ke tuhuma da yi wa 'yan matan ciki 'yan sanda sun wallafa sunayensu a matsayin wadanda a ke nema ruwa a jollo. Kungiyoyin kare hakkin jama'a na ciki da wajen kasar Tanzaniya, kamarsu Human Rights Watch duk sun Allah wadai da dokokin na gwamnatin Tazaniya, inda suka ce haramta wa masu dauke da juna biyu karatun, ya saba wa dokokin duniya, wanda kasar ta Tazaniya ta sanya wa hannu.