1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanarwa kan zaben Laberiya

Salissou Boukari
November 9, 2017

Jam'iyyar dan takarar neman shugabancin kasar Laberiya George Weah ta fitar da wata sanarwa da kakkausar murya inda ta nemi da a farfado da harkokin zaben zagaye na biyu ba tare da bata lokaci ba.

https://p.dw.com/p/2nKH0
Libera, George Weah
Dan takarar neman shugabancin kasar Laberiya George WeahHoto: Getty Images

A ranar Talata da ta gabata ne dai ta kamata a yi zaben tsakanin dan takatara George Weah  da ya zo na daya da kuma mataimakin shugaban kasar ta Laberiya mai barin gado Joseph Boakai da ya zo na biyu a zagayen farko na zaben da ya gudana na ran 10 ga watan Octoba. Kotun kolin kasar ta Laberiya ce dai ta dakatar da harkokin zaben a ranar Litinin, inda ta bai wa hukumar zaben kasar izinin yin nazarin wani kara da dan takarar jam'iyyar Liberte Charles Brumskine da ya zo na uku a zaben ya shigar inda kuma ake ganin binciken ka iya daukan kwanaki da dama ko ma makonni. Jam'iyyar ta Weah ta ce duk da ta na mutunta matakin na kotu amma ta yi kira ga dukannin masu ruwa da tsaki kan harkokin zaben da su gaggauta koma wa bisa hanya.