Zaben fidda gwani a Hampshire
February 12, 2020Talla
Duk da cewar ba da wasu kuri'u masu yawa ya samu nasarar ba, hakan ya karfafa matsayinsa a yunkurin shiga fadar gwamnati ta White House gabanin abokin adawarsa kuma mai sassaucin ra'ayi Joe Biden, da ya zo na biyar.
Pete Bittingieg, dan shekaru 38 da haihuwa kuma tsohon magajin garin South Bend, a Indiana ya zo na biyu, bayan yi wa Sanders pincinkau a zaben fitar da gwani na jihar Iowa a makon da ya gabata.
Sai dai a sauwake Donald Trump ya samu nasarar lashe zaben da mafi rinjayen kuri'u a jam'iyyarsa ta Republican, inda ya doke abokin takararsa William Weld da ke zama tsohon gwamnan Massachusetts da ke makwabtaka.