Kenya: Annobar amai da gudawa a Dadaab
June 6, 2023Kungiyar likitoci na gari na kowa ta Medicine Sans Frontiers reshen gabashin Afirka, na gargadi game da cutar kwalara da ta bulla kuma take ta'adi a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da ke dauke da sama da mutane dubu 300 a yanzu. Galibin wadanda ke zaune a sansanin dai, sun fito ne daga Somaliya da ma wasu makwabtan kasar ta Kenya. Bayanai na nuna cewa akwai kimanin mutane dubu bakwai da 800 da suka kamu da cutar ta kwalara a kasar cikin watan Maris na wannan shekara, inda tuni ma ta yi ajalin 127 daga ciki. A sansanin na Dadaaba kadai ma dai, an samu sama da mutane dubu biyu da 700 wadanda cutar ta kama kawo yanzu. Daraktan kungiyar likitoci na gari na kowa a Kenya, Hassan Maiyaki ya shaida wa DW cewa wannan ne ibtila'in cuta mafi muni da kasar ta gani cikin shekaru biyar da suka gabata kuma hadarin na nuna alamun kara karfi.
Dalilan da ke ta'azzara lamarin dai sun hada ne da rashin tsaftar muhalli da ta jiki da kuma karuwar 'yan gudun hijira da ake samu a sansanin baya ga karancin kudin da kungiyoyi ke bukata. Babban jami'in da ke kula da harkokin lafiya a kungiyar ta kungiyar likitoci na gari na kowa MSF a sansanin na Dadaab Dakta Kapil Sharma ya ce, babban dalilin da ya sanya cutar da ta kwashe watanni bakwai tana ta'adi shi ne batun rashin tsafta. Tun cikin watan Fabarairun wannan shekara ne dai, ma'aikatar lafiya ta Kenyan tare da wasu kungiyoyi ke gudanar da aikin riga-kafin cutar kwalara wato amai da gudawa a sansanoni. Haka ma sun yi aikin fadakar da jama'a, amma kuma masana a fannin lafiya sun ce abin da suka yi bai wadatar ba. A shekarar da ta gabata ta 2022 kasar Kenya ta karbi 'yan gudun hijira kimanin mutum dubu 100, kuma dubu 67 daga ciki sun fake ne a sansanin na Dadaab, abin da ya sa ake nuna damuwa da yawan mutanen da ke wajen.