Sanyawa Sudan ta Kudu takunkumi
May 23, 2015Talla
Mr. Kiir ya ce a wannan hali da ake ciki maganar sanya musu takunkumi ma ba ta taso ba, maimakon haka in ji shi kamata ya yi a maida hankali wajen kawo karshen rikicin da kasar ke fuskanta.
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka ta AU da kuma ta IGAD sun yi barazanar sanyawa Sudan ta Kudu din takunkumi saboda rashin maida hankali wajen kawo karshen rikici tsakanin gwamnati da 'yan tawaye wanda ke cigaba da haifar da cin zarafin dan Adam a kasar.