Sudan ta fara samun Tallafi daga Saudiya
August 7, 2019Talla
Baya ga haka, kasashen biyu, sun ce akwai tsabar kudi na dala miliyan 500 da suka adana a babban bankin Kasar Sudan, don daukar dawainiyar kayayyakin masarufi da zummar rage radaddin da jama'ar da ke cikin bukatar taimako za su amfana. Sudan dai ta kwashi watannnin tana fama da rikici kan samar da gwamnatin hadaka, bayan kifar da gwamnatin Oumar al-Bashir na kusan shekaru talatin.