1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara a sakamakon hari da jirgin Drone

Ramatu Garba Baba MNA
September 14, 2019

Hukumomi a Saudiyya sun tabbatar da labarin kai wa kasar wasu hare-hare da aka yi amfani da samfurin jirgin sama mara matuki a wasu manyan kamfanonin mai.

https://p.dw.com/p/3PbEt
Saudi-Arabien Feuer in der Aramco-Ölaufbereitungsanlage in Abqaiq
Hoto: Reuters

Sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta fitar, ta ce akwai wani bangaren da aka kai harin da aka yi ta jin karar harbin bindigogi sai dai babu karin bayani kan irin asarar da ake zaton harin zai janyo. Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin hannu a harin na wannan Asabar.

Kafafen watsa labarai na kasar sun ci gaba da nuna halin da ake ciki a kamfanonin da aka kai wa wadannan hare-haren. Tuni dai aka soma gudanar da bincike a yayin da ake kokarin shawo kan gobarar. Wannan dai ba shi ba ne karon farko da kasar ke fuskantar hari makamancin na wannan rana.