Sabani ya jagoranci kashe Al-Fagham
September 29, 2019Talla
Rahotanni na nuni da cewar, an kashe Manjo Janar Abdel Aziz al-Fagham ne a ya yin wata ziyara da ya kai a gidan abokinsa da ke Jiddah da ke arewacin fadar da sarkin yake hutu a lokacin bazara.
'Yan sanda sun bayyana cewa an samu rashin jituwa tsakanin dogarin da kuma wani abokinsa mai suna Mamdouh bin Meshaal Al Ali da shi ma ya kai ziyara gidan da mai tsaron sarkin ya je.
A safiyar wannan lahadin ce dai, aka sanar da kashe Manjo Janar Abdulaziz al-Fagham, ta harbin bindiga a birnin Jidda.
Saudiyyar ta mika ta'aziyyarta ga iyalan al-Fagham, tare da nuna hotunansa lokacin da yake tsaron marigayi Sarki Abdullah na masarautar.