Saudiyya: Bincike game da kisan Khashoggi
November 12, 2018Sakataren harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt a yau Litinin zai kai ziyara Saudiyya domin tattaunawa da kuma yin matsin lamba ga yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman dangane da kisan gillar da aka yiwa dan jaridar nan Jamal Khashoggi.
A yayin ziyarar wadda za ta kai shi zuwa kasar hadaddiyar daular larabawa, Hunt zai kuma bukaci karin goyon baya ga yunkurin Majalisar Dinkin Duniya na kawo karshen yakin da ake yi a Yemen.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya ruwaito cewa Yarima Mohammed Bin Salman ya tattauna ta wayar tarho da Simon McDonald jakadan musamman na Firaministar Birtaniya Theresa May game da dangantaka tsakanin Saudiyya da Birtaniya.
Birtaniya dai na bukatar Saudiyya ta bada cikakken hadin kai ga binciken da ake yi kan kisan Jamal Khashoggi.