1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya: Cece-kuce kan yaki da rashawa

Mahmud Yaya Azare RGB
November 6, 2017

Matakin da sabuwar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Saudiyya ta dauka kan yaki da rashawa ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin al'umma kan dalilan daukar matakin da masu sharhi ke cewa akwai lauje cikin nadi.

https://p.dw.com/p/2n7NU
König Salman Bin Abdul Aziz Al Saud und Kronprinz Mohammed Bin Salman Al Saud
Hoto: picture-alliance/abaca/B. Press

Muhawarar kan matakin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta biyo bayan matakin da Yerima mai jiran gado a kasar ta Saudiyya Mohammed bin Salman ya dauka na sallamar wasu masu fada a ji a gwamnati tare da tsare wasu yarimomi goma sha daya dama wasu tsoffin ministoci da ake zargi da handame dukiyar kasa.

Ra'ayoyin ‘yan kasar ya bambamta kan kamen da aka yi tun bayan kafa sabuwar hukumar yaki da cin hancin da yariman ya ce an kafa ne domin ceto masarautar daga almundahana da yai mata katutu. Sarkin ya ce in har an nuna halin ko in kula kan matsalar toh fa kasar ba za ta dore ba.

Wasu daga cikin ‘yan kasar na ganin matakin zai kara daga martabar kasar a idon duniya tare da sanya sauran ma'aikata yin hattara wajen adana dukiyar kasa. Yayin da wasu daga cikin masu sharhi ke cewa da dama daga cikin wadanda aka kora sun kasance wadanda ke adawa da siyasar yariman mai jiran gadon ne. Gwamnatin Saudiyya ta ce wannan sabon kwamiti na da karfin tuhumar duk wani jami'n gwamnati na yanzu ko na baya da ake zargi da aikata ba dai-dai ba.