1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira ga sojin Sudan

Binta Aliyu Zurmi
November 4, 2021

A karon farko kasashen Larabawa sun yi kira ga dakarun sojin Sudan na maida mulki ga farar hula.

https://p.dw.com/p/42YqY
Putsch im Sudan | General Abdel Fattah al-Burhan
Hoto: /AP/dpa/picture alliance

Kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bi sahun kawayensu na kasashen yamma wajen kira ga sojin kasar Sudan da suka karbe iko na su gaggauta maida mulki ga gwamnatin farar hula.

Wannan dai na zuwa ne bayan da a baya kasashen na larabawa da ke da kyakyawar alaka da dakarun sojin Sudan din, ba su yi wata kwakwarar magana a kan karbe ikon da soji suka yi a kasar ba.

A sanarwar hadin gwiwa da suka fidda sun bukaci da a gagauta sakin duk wadanda ake tsare da su a game da wannan batu da ma janye dokar ta baci a kasar.

Amirka ta bukaci Hadaddiyar Daular Larabawa da ta kara matsa kaimi ga sojojin Sudan da su saki hambararen firaminista Abdallah Hamdok daga daurin talala da suke ci gaba da yi mishi a gida.


Al'ummar kasar Sudan na masu adawa da matakin karbe iko da sojojin suka yi lamarin da ya kai su ga hawa tituna domin zanga-zangar lumana da ta yi sanadiyar rayukan wasu daga cikinsu.