Zanga-zangar adawa da tsare Falisdinawa
October 16, 2019Talla
Iyalan fursinonin sun gudanar da zanga-zangar a harabar wani ofishin kungiyar agaji ta Red Cross a birnin Gaza, sun yi kira da a daina gallaza wa fursunonin bisa zargin hannu a ayyukan ta'addanci. Amma kakakin kungiyar ta Hamas ya musanta wadannan zarge-zargen inda ya ce matakin kai samamen da Saudiyya ta yi inda ta kame Falisdinawa fiye da hamsin ciki har da likitoci da manyan 'yan kasuwa, ya biyo bayan sulhun da kungiyar ta yi ne da gwamnatin Iran da yanzu haka ke takun saka da Saudiyyan. An gano yadda fursunoni ke cikin wani yanayi da aka ce ya tauye 'yancin kowanne dan Adam.