Musulmi a Saudiyya sun fara aikin bana
July 29, 2020Talla
An takaita yawan maniyatan da ke aikin hajjin na bana basu da yawa saboda annobar corona da ta yadu a fadin duniya.
'Yan kasar Saudiyya ne kadai da kuma baki daga kasashe kimanin 160 wadanda ke zaune a kasar ta Saudiyya suke gudanar da aikin hajjin ba bana.
A shekarun baya dai musulmi kimanin miliyan biyu da rabi ke hallara a birnin Makka domin gudanar da aikin hajjin wanda ke zama daya daga cikin shikashikan musulunci guda biyar da ake bukatar dukkan musulmi da ke da iko ya halarta akalla sau daya a rayuwarsa.
Alhazan za su kwana yau a Minna kafin su wuce zuwa hawan Arfat a ranar Alhamis.