Saudiyya na koran baƙi 'yan ci-rani daga ƙasarta.
November 15, 2013To a cikin sharhunan jaridun Jamus kan nahiyar Afirka, a wannan makon, za mu fara ne da batun korar baƙi 'yan ci-rani a Saudi Arabiya. Inda jaridar Neue Zürcher Zeitung, ta ce ƙasar Saudiya ta ɗau matakan koran baƙi 'yan ci-rani a wani mataki da ta ƙira wai domin ƙarfafa tattalin arzikinta ne. Bakin da akasari su ka fito daga ƙasashen Afrika da Asiya, sun gamu da fushin mahukuntan Saudiya ne, bayan da aka ba su wa'adi na watanni shida domin su gyara takardunsu na izinin zama. Sai dai su kuma baƙin wasun sun suka ce, suna da halartattun takardu, amma duk da haka an tasa ƙeyarsu.
Daga Afirka dai an bayyana cewa 'yan ƙasashen Somaliya da Habasha da Chadi su ne lamarin ya fi shafa. Sai dai jaridar ta ce, ko da shike Saudiya na son samarwa 'yan ƙasar ta guraben aiki, a matsayin dalilin koran baƙin, amma fa a zahiri da wuya 'yan asalin Saudiya su iya tsayawa su yi aikin da baƙi ke yi, kuma hakan na iya shafar tattalin arzikin ƙasar.
Sai jaridar Süddeutsche Zeitung, ta mai da hankali ne kan batun yaƙi da ta'addanci a ƙasar Kenya. Inda ta ce, bayan harin da aka kai a kasuwar zamani da aka sani da Westgate, gwamnatin ƙasar Kenya ta shirya maida Somaliyawa 'yan gudun hijra kimanin 500,000 izuwa gida. Ƙungiyar Al-shabab ta ƙasar Somaliya, ta ɗauki alhakin harin ta'addanci da ya gir-giza birnin Nairobin Kenya, harin da kuma aka samu zubar da jini. Bisa matakin na mayar da Somaliyawan gida dai, gwamnatin ƙasar Kenya da ƙasar Somaliya, dama hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD wato UNHCR, sun shirya yadda za a aiwatar da shirin na kwashe mutanen.
Yarjejeniyar sulhun Kwango ta ci tura
Ita kuwa jaridar Die Tagezeitung, ta yi sharhinta ne kan taron sulhu tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango. Jaridar ta ce, bayan makwanni da aka yi ana tattaunawa tsakanin wakilan 'yan tawayen M23 da gwamnati da kuma masu shiga tsakani daga ƙasa da ƙasa a birnin Kampala, daga ƙarshe da aka kai lokacin sa hanu sai wakilan gwamnati a tattaunawar su ka ƙi sa hanu kan daftarin da aka cimma. A faɗar kakakin gwamnatin Yuganda Ofwono Opondo, wakilan suna cikin jira, ba tsammani sai jakadan ƙasar Kwango a Yuganda, ya bayyana kuma ya ce yana buƙatar sake bin daftarin da aka tsara, wai ko an canza wani abu da bai sani ba. Kuma bayan haka ne, a wannan ranar wakilan gwamnatin Kwango a tattaunawar da aka yi suka bar ƙasar Yuganda su ka koma Kinshasa.
Kisan gilla bisa kyama, wannan shi ne taken da sharhin jaridar Farankfurter Allgemeine Zeitung ta fara da shi. Jaridar ta ce Eric Bwire ɗaya da ga cikin masu kare haƙƙin 'yan luwadi da maɗigo a ƙasar Yuganda, wanda a yanzu haka ya ke mafaka a ƙasar Jamus, ya samarwa 'yan ƙasarsa da ke ra'ayin irin nasa wata babbar nasara. Inda wata kotu a ƙasar Jamus ta yanke hukuncin bisa ƙarar da ya shigar, kuma ta amince cewa, 'yan luwaɗi ko maɗigo da ke fiskantar barazana a ƙasashensu na asali, suna iya samun mafakar siyasa a ƙasar Jamus.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Pinado Abdu Waba