SiyasaGabas ta Tsakiya
Saudiyya ba za ta daidaita huldarta da Isra'ila ba
August 19, 2020Talla
Sabanin kasar Hadaddiyar Daular Laraba, kasar Saudiyya ta ce ba za ta daidaita dangantakarta da kasar Isra'ila ba, matsayawar ba ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Falasdinu ba.
Ministan harkokin wajen Saudiyya Yerima Faisal bin Farhan ya fadi haka a wannan Laraba yayin wata ziyara da ya kai a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus.
Ya ce dole zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu ya zama abin da kasashen duniya za su aminta da shi. Ya ce idan aka cimma wannan to komai ma mai yiwuwa ne.
A makon da ya gabata ne Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa suka sanar da kulla huldar diplomasiyya tsakaninsu. Daular Larabawa dai ta zama kasar Larabawa ta uku bayan kasashen Masar da Jordan da ta kulla huldar diplomasiyya da Isra'ila.