Saudiyya ta ce tsara kisan Khashoggi aka yi
October 26, 2018A karon farko tun bayan kisan dan jaridar nan na kasar Saudiyya Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyya a birnin istanbul na Turkiyya, mahukuntan Riyad sun amince cewa wadanda suka kashe dan jaridan sun tsara aikata kashe shi ne kawai tun farko ba wai ya mutu ba ne a bisa hadari kamar yadda suka sanar da farko.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis babban mai shigar da kara na gwamnatin Saudiyya ya ce bayanan da suka samu daga mahukuntan Turkiyya ne suka tabbatar masu da hakan.
Kafafen yada labaran kasar ta Saudiyya sun ruwaito cewa ko a jiya Alhamis Yarima Mohamed ben Salmane ya jagoranci a karon farko taron wani kwamiti da ya kafa da zai yi nazarin sake fasalin hukumar leken asirin kasar wacce ake zargin jami'anta ne suka kashe dan jaridar.
Ita ma dai daga nata bangare daraktar hukumar leken asirin Amirka ta CIA, Gina Haspel a jiya Alhamis ta gabatar wa da Shugaba Donald Trump sakamakon ziyarar da ta kai a Turkiyya da kuma tattaunawar da ta yi da masu aikin bincike na kasar Turkiyyar kan batun kisan dan jaridan.