1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus ta sa an dakatar da ziyara dakin Ka'aba

Ramatu Garba Baba
February 27, 2020

Gwamnatin kasar Saudiyya ta dauki matakin hana maniyata ziyara a dakin Ka'aba a matsayin riga-kafi daga yaduwar cutar Coronavirus da ke ci gaba da lakume rayuka a sassan duniya.

https://p.dw.com/p/3YUyb
Haddsch Islamische Pilgerfahrt nach Mekka | Kabaa, Große Moschee
Hoto: picture-alliance/AP Photo/K. Hamra

Annobar Coronavirus da ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya, ta sa gwamnatin kasar Saudiyya daukar matakin dakatar da masu zuwa umara da ziyarar dakin Ka'aba da masallacin Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi da ke garin Madina. Wannan dai na zuwa ne gabanin gudanar da aikin hajji da ke hada kan al'ummar musulmi daga sassan duniya.

Haka kuma, ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar, ta ce ta dauki matakan na ganin ta hana yaduwar cutar inda ta shawarci 'yan kasar da su kiyaye su san irin takun da za su yi a kasashen da annobar ta riga ta bazu. 

Saudiya na daga cikin kasashen da ke fuskantar barazanar yaduwar cutar a yankin Gabas Ta Tsakiya inda kawo yanzu mutum kimanin dari biyu da ashirin suka riga suka kamu da cutar mai kama numfashi.