Saudiyya ta kafa rundunar yaki da ta'addanci
December 15, 2015Talla
Kasar ta Saudiyya ta kafa wannan runduna ta musamman ne tare da wasu kasashen Musulmi da za ta dukufa kan yaki da ta'addanci. Wannan runduna dai ta hada kasashen 34 cikinsu har da kasashen Masar, Pakistan, da Senegal. Sai dai wannan runduna an kafa ta ne ba tare da kasar Iran ba, kuma Saudiyya ce za ta jagorance ta, inda aka kafa cibiyar rundunar a birnin Ryad na kasar ta Saudiyya.