Saudiyya ta kira jakadanta daga Jamus
November 18, 2017Wannan na bangaren nuna rashin amincewarta da kalaman da ministan harakokin wajen Jamus Sigmar Gabrile ya furta inda ya danganta murabus din firaminista Hariri na Labanan da matsin lambar kasar Saudiyya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da firaministan kasar Labanan mai murabus Saad Hariri ya isa a birnin Paris na Faransa a wannan Asabar inda zai gana da Shugaba Emmanule Macron.
Shugaba kasar ta Faransa wacce ke shiga tsakani a cikin rikicin diplomasiyyar da ya barke tsakanin kasashen na Labanan da Saudiyya da ma Iran tun bayan murabus din ba zata da Saad Hariri ya yi a ranar hudu ga watan nan na Nowamba daga kasar Saudiyya, ya gayyato firaministan kasar ta Labanan da iyalansa ne a kasar ta Faransa a wani yinkuri na neman yayyafa wa wutar rikicin ruwa.
Murabus din Hariri daga Saudiyya na ci gaba da haifar da cece-kuce a yankin Gabas ta Tsakiya inda hatta shugaban kasar ta labanan Michel Aoun ya zargi kasar ta Saudiyya da yin garkuwa da firaministan kasar tasa.