Boedeker ya rasu makonni biyu da suka shige
November 30, 2019Talla
Mahukuntan kasar Saudi Arebiya sun sanya wa wani katafaren wurin shakatawa da ke yankin jami'an diplomasiyya a birnin Riyadh sunan wani Bajamushe da ya dauki tsawon shekaru 50 yana yiwa iyalan masarautar hidimar dasa itatuwa.
Tun daga shekara ta 1973 ne dai Boedeker ya ke tsara yadda za a alkinta yanayi na saharan Saudi Arebiya ta hanyar dasa itatuwa, mutumin da ya zartar da manyan ayyuka na dashen itatuwa a titunan Saudiyya masu cunkoso da wuraren shakatawa.