1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta rataye wani dan Pakistan

Mouhamadou Awal BalarabeFebruary 12, 2015

Bayan da ta sami wani dan Pakistan da babban laifi, Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa a kanshi. Ta na aiwatar da irin wannan hukuci a kann masu kisan Kai da fyade.

https://p.dw.com/p/1EaZr
Hoto: vkara - Fotolia.com

Hukumomin Saudiyya sun rataye wani dan Pakistan kai sakamakon yanke masa hukuncin kisa da aka yi bayan da aka same shi da laifin safarar miyagun kwayoyi. Shi dai Babir Isaac, shi ne mutum na 29 da aka aiwatar da hukuncin kisa a kansa a Saudiyya tun daga farkon wannan shekara i zuwa yanzu.

Kungiyoyin duniya da suka himmatu wajen kare hakkin dan Adama suna ci gaba da yin tir da dokokin na Saudiyya da suka tanadi kisa idan aka same mutum da wani mummunan laifuka ,ciki har da fyade da kisan kai da yin ridda da kuma saye ko sayar da miyagun kwayoyi.

A watan Satumba na shekarar da ta gabata, wani kwararren jami'i na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana fargabar game da yadda shari'a ke gudana a wannan kasa, tare da yin kira ga Saudiyya da ta jingine shari'ar musulunci wajen yanke hukunci.