1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta sallami 'yan cirani dubu 370

March 20, 2014

Mahukuntan Saudi Arabiya sun sallami baki 'yan cirani kimanin dubu 370 wanda suka shiga kasar kuma su ke aiki ba tare da cikakkatun takardun izinin yin hakan ba.

https://p.dw.com/p/1BTWB
Saudi-Arabien König Abdullah
Hoto: picture-alliance/ZB

Ma'aikatar cikin gida ta Saudiyyan ta ce 'yan ciranin sun fito ne daga kasashe daban-daban na duniya kuma an maida su zuwa kasashensu a tsakanin watanni biyar din da suka gabata, kazalika ma'aikatar a wannan Alhamis din ta ce ta na tsare da wasu karin mutane dubu 18 kuma nan gaba kadan za a maida su kasashensu.

Tuni dai masu kare hakkin bani adama na kasa da kasa suka fara kokawa dangane da wannan mataki da Saudiyyan ta dauka domin a cewarsu 'yan ciranin na shiga halin kunci a wuraren da ake tsaresu, ko da dai Saudin ta musanta hakan inda ta kara da cewar ta na sallamar bakin haure ne a wani mataki na samawa 'yan kasarta aikin yi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal