1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Saudiyya ta sasanta da Qatar

January 5, 2021

Saudiyya wacce ta kakaba wa kasar Qatar takunkumi a baya, ta dawo da alaka a tsakanin su. Saudiyyar ta hada kai ne da wasu kasashen yankin Gulf wajen daukar matakin.

https://p.dw.com/p/3nXNM
Katar | Salman bin Abdulaziz in Katar
Hoto: Bandar Algaloud/Saudi Kingdom Handout/AA/picture alliance

Shugabannin kasashen Larabawa, wadanda ke taron neman warware takunkumin da aka kakaba wa kasar Qatar, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar dorewar hadin kai da zaman lafiya domin ci gaban yankin.

Yerima mai jiran sarautar Saudiyya, Muhammad bin Salman, shi ne ya sanar da hakan a birnin Al-Ula.

Yeriman na Saudiyya ya ce alamu sun tabbatar da bukatar hadin kan kasashen na yankin Gulf domin fuskantar matsalolin da suka yi musu dabaibayi.

A shekara ta 2017 ne dai kasar ta Saudiyya ta jagoranci wasu kasashen yankin, wajen yanke wasu huldodi da Qatar, inda suka zarge ta da dasawa da Iran da da ma taimaka wa harkokin ta'addanci, abin kuma da kasar ta Qatar ta sha musantawa.