Saudiyya ta sassauta dokar corona a manyan masallatan kasar
October 17, 2021Talla
Mahukuntan Saudiyya sun sassauta matakan kariya da aka sanya a kasar don hana yaduwar cutar corona inda aka soke dokar bayar da tazara a tsakanin masallata a yayin gudanar da ibada a masallacin Makka dana Madina, duk da cewa, an nemi masu son yin ibada a masallatai, su kasance wadanda suka kammala allurar riga-kafin corona guda biyu.
Umarnin ya soma aiki daga wannan Lahadin. Mahukuntan na Saudiyya, sun dauki matakin sassauta matakan kariyar, bayan da aka sami raguwar masu kamuwa da cutar mai sarke numfashi. Mutum fiye da dubu takwas annobar corona ta kashe daga cikin sama da dubu dari biyar da suka kamu da cutar a kasar.