Jamal Kashoggi ya rasu a ofishin jakadancin Saudiyya
October 20, 2018Sanarwar ta kara da cewar Kashoggi ya rasa ransa ne biyo bayan kaurewar kokawa tsakanin sa da jami'an da ya gana dasu a ofishin jakadancin, tuni dai ofishin mai gabatar da kara a Saudiyyan ya bada umarnin tsare mutane 18 'yan asalin kasar ta Saudi Arabiya bayan sallamar mataimakin shugaban hukumar leken asirin kasar Ahmed Asiri tare da mashawarcin masarautar kasar Saud al-Qahtani daga aiyyukansu nan take.
Kafin rasuwarsa Kashoggi ya yi fice wajen sukar lamirin Yarima Muhammad Bin Salman. A nata bangaren gwamnatin kasar Turkiyya na cigaba bayyana yadda mutanen da suka kashe 'dan jaridar suka daddatsa gabobinsa yayin da suke gana masa azaba a ofishin jakadancin na Saudiyya.
Tuni dai fadar White House ta aike da sakon ta'aziyyar ga iyalai da kuma aminan Jamal Kashoggi.