Saudiyya: Ba mu da hannu a harin 9/11
September 8, 2021Talla
Sai dai wata sanarwa daga ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Washington na cewa "Duk wani zargin da zai nuna hannun Saudiyya a hare -haren 11 ga Satumba, karya ne." a cewar sanarwar.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Shugaba Joe Biden ya umarci a sake muhimman takardun sirrin da aka kebe kan harin nan da watanni shida, sakamakon matsin lamba da ya ke fuskanta daga iyalan mutane sama da 3,000 da harin ya kashe. A ranar Asabar 09/09/2021 ake cika shekaru 20 da kungiyar al-Qaida ta kai harin 9/11/2001, ranar da ke zuwa wata guda bayan janye sojojin Amirka a Afganistan tun bayan shigarsu daukar fansa kan Osama bin Laden a 2001.