1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Fargabar koma baya a cininkin mai

November 4, 2018

Saudiyya da kasashe masu arzikin mai na shirye-shiryen ninka yawan mai da za su rika hakowa, bayan koma baya da Iran za ta iya samu ta fuskar makamashi.

https://p.dw.com/p/37d68
Saudi-Arabien | Stopp aller Öltransporte durch die Meerenge von Bab el-Mandeb im Roten Meer
Daya daga cikin matatun mai a SaudiyyaHoto: Reuters/File Photo/A. Jadallah

Masu nazarin harkokin arziki a duniya, sun ce Saudiyya da sauran kasashe mambobin kungiyar OPEC na shirye-shiryen ninka yawan mai da za su rika fitarwa, duk da rashin tabbas da ake gani a kasuwar makamashin.

Yunkurin na zuwa ne yayin da Amirka ke shirin kakaba wa Iran takunkumai, ciki har da na bangaren mai. Masanan na cewa hakan zai shafi cinikin man Iran, wadda ke hakar ganga miliyan biyu da dubu 500 a kullum.

Idan kuma takunkumin na Amirka ya tabbata a ranar Litinin kamar yadda Shugaba Trump ya fada, to kasar za ta koma hakar ganga miliyan daya da doriya ne a yini guda. Sai dai ga dukkan alamu dai kasar Saudiyya ce za ta maye gibin mai na Iran, bayan tabbatuwar takunkumin.