1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya za ta budewa Katar iyakokinta

Abdul-raheem Hassan
January 5, 2021

A wani mataki na kawo karshen rikicin diflomasiyya da ya raba tsakanin kasashen biyu makotan juna na yankin Gulf, Saudiyya za ta bude wa Katar iyakokinta bayan killace su kan zargin taimakon ta'addanci.

https://p.dw.com/p/3nVv6
Katar | Salman bin Abdulaziz in Katar
Hoto: Bandar Algaloud/Saudi Kingdom Handout/AA/picture alliance

Tun a tsakiyar 2017 ne iyakar Katar da Saudiyya ta kasance a rufe, bayan da kawayenta Saudiyyar da Masar da hadaddiyar daular Larabawa da Bahrain suka sa mata takunkumi kan zargin taimakawa ta'addanci da kuma kawance da Iran.

Babu tabbacin ko akwai wasu sharuda da Katar din ta cike kan a cimma wannan mataki, amma dage wa Katar wannan takunkumin zai ba wa Sarkin Sheikh bin Hamad Al Thani damar halartar babban taron shugabannin yankin Gulf da Sarkin Saudiyyar zai jagoranta a wannan talatar.