FIFA 2034: Saudiyya ce mai masaukin baki
December 11, 2024Kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa na cece-kuce a kan Saudiyyan, dangane da rashin kiyaye hakkokin kwadago da 'yancin fadin albarkacin baki da ma na masu neman jinsi daya a kasar. A cikin tsarin zabe da Hukumar Kwallo ta Duniya FIFA ta yi Saudiyyan ta samu maki sama da 419 daga cikin 500, abin kuma da ya ba ta rinjaye gagarumi. Duk dai da hujjojin da kungiyoyi suka gabatar dangane da batun take hakkin dan Adam, hukumar ta FIFA ta ce Saudiyyan na matsakaicin mataki ne na hadari. Lina al-Hathloul shugabar wata kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam a Saudiyya ta ce ba a iya samun wadanda ke magana da ke sukar gwamnatin kasar, sai dai kawai yaba mata da za a yi saboda amfani da kalaman da ke sukar hukumomi ka iya aika wa da mutum gidan yari kai tsaye. Ta dai kai ga yin hayar wasu kungiyoyin lauyoyi biyu da suka hadu suka kira kansu AS&H a Saudiyya da suka samar da rahoto mai zaman kansa, wanda ya bai wa Hukumar Kwallo ta Duniya FIFA damar iya tantance batutuwa masu nasaba da hakkokin dan Adam din.
A shekara ta 2016 hukumar FIFA ta amince da wasu ka'idodjin Majalisar Dinkin Duniya a kan kasuwanci da hakkokin dan Adama, inda a wancan lokaci aka yaba mata da hakan. Shugaban sashen kare hakkokin kwadago gami da wasanni a kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International Steve Cockburn ya yi amannar cewa, tsarin da aka bi wajen zabar masu daukar nauyin gasar kwallo ta duniya a 2030 da 2034 ya bai wa hukumar FIFA damar kauce wa wasu daga cikin nauye-nauyen da ke kansa musamman a kan wannan batu. Kuma rahoton har ila yau, an takaita shi ga samun nazarin fannonin kare hakki 22 a duniya wanda FIFA da Hukumar Kwallon Kafar ta Saudiya SAFF ne suka yi. An ma kauce wa batun 'yancin fadin albarkacin baki da bacewar mutane da ake zargin hukumomi da aikatawa da tauye hakkin jama'a, maimakon hakan rahoto ko bincike ya takaita ne kawai a kan dokokin cikin gida na kasar ta Saudiyya. Dokokin dai a cewar masana, sun ci karo da tsarin kiyaye hakkoki na duniya musamman 'yancin mata da na masu neman jinsi guda da ma yadda ake yi wa ma'aikata baki 'yan ci-rani.
Batun kare hakkin dan Adam a Saudiyyan ya kuma dubi kisan baki 'yan ci-rani da adadinsu ya kusa mutane 900, a kasar da ke da irin wadannan mutane da yawansu ya kai kimanin miliyan 13 da dubu 400 da kuma ke kan karuwa a daidai lokacin da take shirin gina sababbin manyan filayen wasanni 11 da kuma sake kwaskware hudu da take da su nan da shekaru 10. Kafin dai Saudiyya ta samu damar daukar bakuncin wasan Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa ta Duniya a 2034, alkaluman da aka tattara sun nunar da cewa akwai 'yan kasar Bangaladash da ke aikatau su 884 da aka kashe a tsakanin watan Janairu zuwa Yulin wannan shekara. Wata bukatar karin haske da DW ta gabatar ga hukumomin Saudiyya game da zarge-zargen take hakkin dan Adam la'akari da batu na shirya gasar ta 2034, ba ta samu amsa ba. Haka ma a cikin wata hirar da kamfanin dillancin labaran Reuters ya yi da Hammad Albalawi da ya shirya zaben kasashen da suka yi takarar gasar ta 2034, nan ma jami'in ya kauce wa wannan matsala da ake zargin Riyadh din da aikatawa.