1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya za ta sayer wa Saudiyya makamai

Abdul-raheem Hassan
July 18, 2023

Masarautar Saudiyya ta amince da sayen jiragen yaki marasa matuka daga Turkiyya, a wani mataki na inganta matakan tsaro cikin gida.

https://p.dw.com/p/4U5OY
Mohammed bin Salman da Recep Tayyip Erdogan
Hoto: Ozan Kose/AFP/Getty Images

Yarjejeniyar sayer da makamann na daya daga cikin kwangiloli da dama da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kulla a daidai lokacin da Ankara ke cin gajiyar sabunta huldar diflomasiyya a baya-bayan nan da manyan ƙasashen Larabawa na yankin Gulf.

Kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna a fannoni da dama ciki har da batun makamashi da zuba jari kai tsaye da kuma masana'antun tsaro.

Saudi Arabiya za ta mallaki jiragen da nufin inganta shirye-shiryen sojojin masarautar da kuma karfafa tsaronta da kuma masana'antu, in ji Ministan Tsaro Yarima Khalid bin Salman Al Saud a cikin wani sakon Twitter a ranar Talata.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ce Erdogan da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman sun halarci bikin rattaba hannu kan kamfanin tsaron Turkiyya Baykar da ma'aikatar tsaron Saudiyya.

Wani jami'in Baykar ya ki cewa komai kan girma da darajar cinikin makaman da kaashen biyu suka kulla. Saudi Arabia ita ce kasa ta shida da ta sayi samfurin irin wannan makami na jirage marasa matuka daga Turkiyya. Adadin kasashe 30 ya zuwa yanzu sun amince su sayi jirage marasa matuka samfurin TB2 da kudinsu ya kai darajar biliyan daya da 200 a shekarar 2022.