Saudiyya za ta wajabta rigakafin corona
May 19, 2021Talla
Dokar za ta shafi ma'aikatu masu zaman kansu da wuraren motsa jiki da makarantu, kowa sai ya nuna shedar yin rigakafin kafin ya samu damar shiga. Sabbin dokokin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da hukumomin Saudiyyar suka umarci ma'aikatan da suka yi rigakafin ne kadai za su komawa bakin aiki.
Bayan shafe shekara guda ba wanda yake fita wajen Saudiyya, yanzu gwamnati ta dage takunkumin hana fita kasashen ketere ga wadanda suka yi rigakafin. Yayin da kasar ta ba da sharudan yin rigakafin ga maniyyata da ke son sauke faralin aikin hajjin bana.