1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya za ta yaki ta'addanci a duniya

November 27, 2017

Masarautar Saudiyya ta ce za ta yaki tare da kakkabe 'yan ta'adda a duk inda suke a duniya. Kasar ta sha alwashin hakan ne a taro kan yaki da ta'addanci da manyan kasashen Musulmi ke yi.

https://p.dw.com/p/2oJ9e
Islamic Military Counter Terrorism Coalition Riad
Hoto: Reuters/B. Algaloud

Yerima Muhammad bin Salman na kasar Saudiyya, ya lashi takobin kakkabe 'yan ta'adda sai ya ga iyakarsu a duk inda suke a duniya. Yerima bin Salman ya fadi hakan ne yayin da wakilan manyan kasashen Musulmai 40 ke halartar wani taro irinsa na farko kan hadin kai don yakar ta'addanci a masarautar.

Taron da ya hada ministocin tsaron kasashen na Musulmi da wasu manyan jami'ai, na zuwa ne yayin da ita babbar kawar Amirka wato Saudiyyar ke jagorantar fatattakar mayakan IS a kasashen Iraki da Siriya. Kasashen da suka hadun dai galibinsu, kasashe ne 'yan Sunni, kuma manyan kasashen Musulmi masu akidar Shi'a irinsu Iran da Iraki da Siriya dai ba su da wakilci a wannan taro.