A cikin shirin za a jin kasar Isra'ila ta gargadi dubban bakin haure 'yan Afirka da su gaggauta ficewa daga kasar cikin kwanaki 90, ko su fuskanci dauri a gidan yari, batun da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka ce yayi hannun riga da dokar kasa da kasa.