Talla
A cikin shirin za ku ji shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan ya soki lamirin tarayyar Turai kan goyon bayan kungiyar PKK. Yayin da sojojin Kurdawa su ka sanar da yunkurin kwato garin Raqqa, a waje guda kuma fararen hula na ta ficewa da birnin Hamamal Alil a kudancin Mosul bayan da sojojin Iraqi su ka karbe ikon garin daga yan IS.