A cikin shirin za a ji cewa shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya karrama MKO Abiola da lambar yabo mafi girma ta kasar a sabuwar ranar da aka ware don raya demokaradiiya, lamarin da ya sha yabo daga mukarabban marigayin. Ita kuwa majalisar dokokin Nijar ta nemi kotun tsarin mulki ta fayyace matsayin Hama Amadou.