Sauyin yanayi ya jawo karancin abinci a duniya
September 11, 2018A rahoton da ta fitar a wannan Talata Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar an samu karuwar mutane milliyan 821 a shekara 2017 wadanda ke da bukata ta abinci sosai, idan aka kwatanta da mutane milliyan 804 da aka samu a shekarar 2016.Yayin da aka gano cewar kasar Afrika ta Kudu ita ce kasa da tafi kowacce yawan masu fama da yunwa a wani sako da David Beasley shugaban hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ya fitar.
Binciken rahoton ya gano cewar sauyin yanayin ya yi wa wasu albarkatun gona illa inda yake rage samar da alkama da shinkafa da masara. kuma ana tsammanin tsanantar yanayin a gaba idan ba a dauki mataki akai ba.
Haka zalika a shekaru uku da suka gabata duba da irin kunci da aka shiga na yunwa an kirayi hukumomi da su taimaka wa wadanda suke da bukatar taimako musamman mata da kananan yara na al'ummar da canjin yanayin ya shafa.