1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Scholz da Putin sun tattauna, karon farko cikin shekaru biyu

Abdullahi Tanko Bala
November 15, 2024

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin sun tattauna a karon farko cikin shekaru biyu a cewar kakakin gwamnatin Jamus. Hakan na zuwa ne bayan nasarar Donald Trump a zabenAmurka

https://p.dw.com/p/4n3tG
Vladimir Putin da Olaf Scholz

Kakakin gwamnatin na Jamus ya ce Scholz da Putin sun yi tattaunawa ta tsawon awa guda.

An nruwaito cewa Scholz ya bukaci Putin ya shiga tattaunawa don samun zaman lafiya mai dorewa da Ukraine.

Haka kuma kakakin gwamnatin ya ce Scholz ya tattauna da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy, kuma shugaban gwamnatin na Jamus ya jaddada kudirin kasarsa na ci gaba da taimaka wa Ukraine komai tsawon lokaci.