1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Scholz ya ba da sanarwar sabon taimako ga Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
December 2, 2024

Tallafin miliyan 650 na Euro da Olaf Scholz ya sanar a Kiyv na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Ukraine ke fuskantar koma baya a fagen yaki, kuma ake fargabar katsewar tallafin Amurka idan Donald Trump ya kama aiki.

https://p.dw.com/p/4neOn
 Scholz na Jamus ya kai wa Zelensky na Ukraine ziyarar ba-zata
Scholz na Jamus ya kai wa Zelensky na Ukraine ziyarar ba-zataHoto: Max Zander/DW

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi alkawarin samar da sabon tallafin da ya kai miliyan 650 na Yuro  ga kasar Ukraine don ta samu karfin tinkarar Rasha da ta mamaye ta tun shekaru biyun da suka gabata. A lokacin wata ziyarar ba zata da ya kai a birnin Kiyv, Scholz ya ce kasarsa Jamus za ta ci gaba da kasancewa muhimmiyar kafa ta taimaka wa Ukraine a fannin tsaro a nahiyar Turai. Dama dai wannan balaguro na kwana guda na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Ukraine ke fuskantar koma baya a fagen yaki, kuma a lokacin da ake fargabar katsewar tallafin daga Amurka idan Donald Trump ya yi rantsuwar kama aiki.

Karin bayani:  Yakin Ukraine na kara yin muni

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi amfani da wannan dama wajen nuna cewa kasarsa na bukatar karin makamai masu cin dogon zango, da kuma tabbacin samun tsaro daga kungiyar tsaro ta NATO kafin yiwuwar zama kan teburin tattaunawa da kasar Rasha. Sai dai shugaban gwamnatin Jamus ya jaddada cewar kasar ba za ta ba wa Ukraine makamai masu linzami masu cin dogon zango ba, yana mai bayanin cewa yana son kauce wa takun saka da Moscow.

Karin bayani:  Ya Koriya ta Arewa za ta sauya yakin Ukraine?

Dama dai a yanayi na tinkarar zaben 'yan majalisar dokokin da za a yi a ranar 23 ga watan Fabrairu a Jamus, Scholz na tallata kansa a matsayin shugaban da ke neman tabbatar da zaman lafiya kuma mai taka-tsantsan don kauce wa barkewar rikici tsakanin kasashen Yamma da Rasha.