'Yan adawa sun lashe zaben kananan hukumomi a Senegal
January 25, 2022Talla
A manyan birane kasar irinsu Dakar da Thiess hadin gwiwar jam'iyyun siyasar da ke yin mulkin sun rasa mazabu da dama masu mahimmanci a gaban jam'iyyun siyasar masu hamayya da gwamnatin wadanda suka hada da na Usman Sankon. Wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugaban kasar da ke tafe. Wannan zabe ana yi masa kallon zakaran gwajin dafi ga zaben na shugaban kasar da za a yi a shekara ta 2024 a Senegal din.