Senegal: Khalifa Sall ya rasa rigar kariyarsa
November 26, 2017Talla
Khalifa Sall da ke a matsayin babban mai adawa da shugaban kasar Macky Sall an zabe shi a matsayin dan majalisar dokoki a lokacin da yake gidan kurkuku, kuma cire masa rigar kariyar zai bada damar a yi masa shari'a kan abubuwan da ake tuhumarsa da aikatawa. Yayin cire rigar kariyar an samu 'yan majalisa na bangaren masu rinjaye 125 da suka kada kuri'ar amincewa, yayin da 27 suka nuna adawarsu ga cire rigar kariyar ta Khalifa Sall.
Magajin garin birnin na Dakar da sunan mahaifansu yake daya da shugaban kasar dai ba su da wata dangantaka ta dan uwantaka. Ya kasance babban mai adawa da shugaban kasar, wanda magoya bayansa ke cewa ba komai ba ne illa bita da kulli na siyasa.