1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

290310 Senegal Präsident Wade

April 4, 2010

Abdoulaye Wade yana alfahari da irin cigaban da ƙasarsa ta samu cikin shekaru 10 na mulkinsa

https://p.dw.com/p/MmsM
Hoto: DW

Shekaru 10 da suka gabata nedai aka zaɓi Abdoulaye Wade zuwa matsayin shugaban  ƙasar senegal dake cika shekaru 50 da samun 'yancin kai daga mulkin mallaka na ƙasar Faransa. Tsawon waɗannan shekaru na mulki ko yaya yake ji kuma  wace irin rawa za'a iya cewar ya taka wajen inganta rayuwar  al'ummar ta Senegal.

" A lokacin da na koma gida da dare , dukkan mutane sun  sun watse ni ɗaya kachal na rage, sa'annan  ne na tambayi kaina, wannan gaskiya ce ko  kuma mafarki nake ?"

 Shugaba Abdoulaye wade kenan a lokacin da yayi nasarar zaɓe. Kuma har ya zuwa wannan lokaci shugaban Senegal yakan yi mamakin cewar, a tun wancan lokacin ma ba mafarki yakeyi ba, idan ya tuna da wancan ranar cikin watan Maris na shekarata 2000. Domin nan take ya samu kira ta waya daga wajen  mai bashi shawara na tsawon lokaci kuma tsohon shugaban Senegal na wancan lokaci, Abdou Diouf..

"...domin fada maka cewar, ka samu nasara Ablaye. Na so shida maka ne kafin in faɗawa kafofin yada labaru. Ina tayaka  murnar lashe zaɓe".

Wade ya cimma, abunda shugabannin kasashen Afrika kalilan ne zasu iya kaiwa ga hakan.Bayan kasancewarsa shugaban adawa na tsawon shekaru 26, al'ummomin senegal sun zaɓeshi  a matsayin shugaban ƙasa. Wanda ya kawo karshen mulkin kama karya nashekaru 40 na   masu ra'ayin gurguzu a Senegal.

"Kafin wannan lokaci  dai na kan yiwa siyasa kallon wasa. Na kan faɗawa kaina kullum cewar, samun nasara ko kuma faɗuwar zaɓen, bazai zame abun nadama ba. Amma a hankali na fara tunanin irin fatan da jama'a ke dashi akai na, a wannan lokaci ne nima na fahinci irin hakki daya rataya a wuyana"

A yanzu haka dai shekaru 10 kenana da shugabancin Abdoulaye wade a senegal, sai dai ra'ayi ya banbanta dangane da yadda yake tafiyar salon mulkinsa. Ga magoya bayan  aƙidarsa ta jari hujja dai , ya kasance ɗan siyasa mai basirar gaske, ayayinda 'yan  adawa  ke masa kallon makwaɗaicin shugaban ƙasa.

 A bayyane take dai, Wade mutum ne mai son yawaita fitowa kafafan yada labaru yana bayanai, musamman dangane da  ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar a cikin ƙasar. Alal misali ya cimma nasarar kare ƙasar daga shigowa da abinci daga ketare, aƙarkashin wani shiri na musamman na kare yunwa da samar da abinci mai gina ciki.

Monument der afrikanischen Wiedergeburt: Statue in Dakar, Senegal Flash-Galerie
Mutum-mutumin cika shekaru 50Hoto: AP

"A yau  muna da kusan dukkanin abinci da muke bukata, ba ma bukatar shigowa dasu. Wannan kuwa babbar nasara ce, wanda yasa babban sakaren Majalisar Ɗunkin Duniya ya taya ni murna. Kuma mun tabbatar da cewar, a shekaru masu zuwa, zamu samu bunƙasar amfaninmu, har ma mu fitar dasu  zuwa  kasuwannin ketare. ketare"

to sai dai akwai korafe korafen cewar mafi yawa da cikin mazauna karkarar Senegal na rayuwa hannu baka hannu ƙwarya sakamakon talauci. Matsanancin talauci ya jagoranci bin ɓarauniyar hanya ta cikin ruwa zuwa turai, tsakanin matasan kasar. Amma abu mafi muni shine rashawa da ya yi katutu inji Baye Diagne wani masanin tattali a birnin Dakar...

Flash - Galerie der Präsidentenpalast in Dakar
Fadar shugaban ƙasaHoto: DW

" Komai ya daɗa lalacewa fiye da ba. Kafin wannan gwamnatin, muna da tsohuwar gwamnati malalaciya wadda ta talauce. Amma a kalla batayi sata ba. Amma  a yau muna da gwammantin gaggawa wadda ke amfani da arzikin ƙasa wajen azurta kanta"

A yanzu haka dai Abdoulaye Wade yana shirin sakeyin takara a zaɓen da zai gudana a shekara ta 2012, idan Allah ya kaimu.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

.

Edita: Abdullahi Tanko Bala