Senegal na bukin shekaru 50 da samun 'yanci
April 4, 2010Talla
Shugaba Abdoulaye Wade na Senegal, ya sanar da cewar ƙasarsa zata karɓe sansanonin sojin dake hannun tsohuwar uwargijiyarsu Faransa. Wasu na ganin cewar shugaban Senegal ɗin ya ambaci wannan batu ne domin burge 'yan ƙasar, adaidai lokacin da ya ke daɗa samun suka da adawa dangane da kaddamar da wani mutum-mutumin mai siffar mace,namiji da jariri a bukin cika shekaru 50 da samun 'yancin kai daga turawan Faransa. Dubban Al'ummomin Senegal ɗin ne dai a jiya, suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da gina mutum-mutumin, wanda acewarsu almubazzaranci ne da dukiyar ƙasa .
Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita Abdullahi Tanko Bala