Senegal: Shirin sauya kudin zabe
April 19, 2018Talla
'Yan sandan sun aiwatar da kame-kamen 'yan adawan cikinsu har da tsohon firaministan kasar Idrissa Seck da Malick Gakou wani kusa a bangaran 'yan adawan sannan da shugaban jam'iyyar Mouvement Agir Thierno Bocoum kaman yadda jam'iyyunsu suka tabbatar. Shi dai tsohon firamonistan kasar ta Senegal Idrissa Seck ya jagoranci gwamnatin kasar ne daga 2002 zuwa 2004 a karkashin jagorancin Shugaba na wancan lokacin Abdoulaye Wade. Masu zanga-zangar dai sun kafa shingaye a tsakiyar wani titi da ke zuwa majalisar dokokin kasar inda za a tattauna batun sauya kundin tsarin zaben.