Senegal ta kira jakadanta a Katar zuwa gida
June 7, 2017Kasar Senegal ta sanar da cewa ta bukaci jakadanta a kasar Katar da ya dawo gida a wani mataki na nuna goyon baya ga matakin kasar Saudiyya da wasu kasasashen Larabawa na katse huldar diplomasiyyarsu da kasar ta Katar a bisa zargin tallafa wa kungiyoyin 'yan ta'adda da yin katsalandan a harkokin cikin gidajensu da kuma yin mu'amala da kasar Iran.
A cikin wata sanarwa da ministan harakokin wajen kasar ta Senegal ya fitar a wannan Laraba, ya ce sun bukaci jakadan nasu da ya dawo gida har zuwa yadda hali ya yi a nan gaba. Sanarwar ta kara da cewa kasar Senegal ta damu sosai da halin da ake ciki a yankin Golf, dan haka take goyon bayan matakin da kasashen Saudiyya daMasar da Bahrain da Daular Larabawa suka dauka na raba gari da kasar ta Katar.
A ranar Litinin da ta gabata ce dai kasashen hudu suka katse huldar diplomasiyyar tasu da kasar Katar kafin daga bisani kasashen Yemen da Mauritaniya da kuma Maldibas su bi sahunsu wajen raba gari da Doha.